<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>341</hymn_number>
<title>Ya Ubangijinmu, Dube Mu Duk Yanzu LW341</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Ubangijinmu, dube mu duk yanzu
 A gabanka.
 Sarkin sarakuna, mai iko duka kuwa,
 Karƃi sujadarmu, Ubangiji.

[V2]
 2) Roƙonka mu ke yi don masu mulkinmu,
 Ka cece su.
 Tsawanta ransu kuwa, su ma a zuciyarsu
 Su nemi fuskarka, Ubangiji.

[V3]
 3) Daidaita hanyarsu cikin sarauta fa,
 Ka riƙe su.
 Ba su albarkarka, girma da lafiya,
 Iko da nasara, Ubangiji.

[V4]
 4) Tuna da ƙasarmu, ka san bukatarmu
 A duniyan nan.
 Kai ne Mai Cetonmu, kai ne shugabanmu,
 Bishe mu duk yanzu, Ubangiji.</lyrics>
</song>